ABNA24 : Har ila yau, ya ci gaba da cewa; Kasashen Iran da Turkiya da suke a matsayin manyan kasashen yankin gabas ta tsakiya a kodayaushe suna fuskantar kiyayya, don haka babu wata hanya a gabansu da ta wuce su zurfafa alakarsu domin samun galaba akan makiya da makarice-makirce.
Shugaban kasar ta Iran ya ci gaba da cewa; An gina alakar Iran da Turkiya ne akan ginshiki mai karfi don haka, duk wasu abubuwa marasa dadi da suke faruwa ba su taba girgiza wannan alakar ba.
Kyakkyawar makwabtaka, al’adu daya, girmama juna, manufofi guda da tsaro da zaman lafiya suna cikin ginshikan wannan alakar, in ji shugaban kasar ta Iran.
Shugaban na kasar Iran ya bayyana fatansa na ganin cewa taron na jiya ya amfanar da kasashen biyu ta fuskoki da dama.
342/